Tambaya:
Mene ne hukuncin taya musulmi murna da ranar Juma'a? Domin yanzu a al'adar , mutane suna aika saƙonni ta wayoyin salula suna taya murna da kalmomin kamar "Juma'a mai albarka" ko "Juma'a mai kyau".
Amsa Taƙaitacciya:
Taya murna da ranar Juma'a da kalmar "Juma'a mai albarka" ba ta shar'anta ba maana bashi cikin sunnah. Amma idan musulmi ya yi wa ɗan'uwansa addu'a a ranar Juma'a da niyyar ƙarfafa zumunci, saka farin ciki, ko neman lokacin amsar addu'a, babu laifi .
Cikakken Amsa:
Darajar Ranar Juma'a:
Babu shakka ranar Juma'a rana ce mai daraja ga musulmi. An samo hadisi daga Ibn Abbas Allah ya yarda da su, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"Wannan rana ce ta idi da Allah ya ba wa musulmi. Duk wanda ya halarci Sallar Juma'a, ya yi wanka. Idan akwai turare, sai ya shafa. Kuma ku yi amfani da asuwaki." (Ibn Majah 1098) Albani ya inganta hadisin a Sahih Ibn Majah.
Hukuncin Taya Murna da Kalmar "Juma'a Mai Albarka":
An halatta taya murna a lokutan Idi da suka hada da Idi Alfitri(karamar Sallah) da na Layya,(babbar Sallah) kuma sahabbai sun yi hakan.
Amma ba a samo ruwaya daga sahabbai ko Manzon Allah (S.A.W) cewa sun kasance suna taya juna murna a ranar Juma’a ba, duk da sanin darajarta.
Ra'ayoyin Malamai:
Sheikh Salih Al-Fawzan ya ce:
"Ba a samo cewa sahabbai sun kasance suna taya juna murna da ranar Juma’a ba. Kada mu kirkiro abin da ba su yi ba."
Sheikh Sulaiman Al-Majid kuma ya ce:
"Ba sharia bace taya murna da ranar Juma’a kamar yadda wasu suke cewa 'Juma’a mai albarka.' Wannan yana cikin addu'o'i da ambato wanda aka iyakance shi da abin da aka ruwaito daga shari'a. Idan da wannan yana da alheri, Manzon Allah da sahabbai za su riga mu yin hakan."
Amma idan mutum ya yi wa ɗan'uwansa addu’a da niyyar ƙarfafa zumunci ko neman lokacin amsar addu'a, babu laifi a hakan.
Allah Yasa mudace
Muhammad Idris Kumbash
Post a Comment