Ma'anar Zakatil
fitr/Zakkar fidda kai
Zakkar Fidda kai wata
sadaka ce da ake wajabta wa musulmi yayin da ya kammala Azumin Ramadan, kuma an
kira ta da Zakatil Fitir ne saboda tana wajabane yayin da musulmi suka kamala
Azumin Ramadhan Ta hanyar ganin watan Sallah.
Hukuncin Zakkar Fidda
kai
An rawaito daga Ibn Abbas (RA) yana cewa:
"Manzon Allah (SAW) ya wajabta Zakkar Fiddakai domin ta
tsarkake mai Azumi daga batanci da rashin da’a, kuma ta zama Abinci ga Talakawa
da Miskinai. Wanda ya bayar da ita kafin a fita sallar Idi, to, shine yafitar da zakkar ingan tacciya, amma wanda ya bayar da
ita bayan sallar Idi, to, sadaka ce kawai daga cikin sauran
sadakoki." Maana be sauke wajibin
da kekanshi ba na zakkar fidda kai.
(Ana samun wannan hadisin a cikin Sunan Abu Dawud
1371).
Lokacin da ake fitar
da Zakkar Fidda kai
Zakkar Fidda kai tana
zama wajibine da zarar rana ta faɗi a ranar ƙarshe ta watan
Ramadan kuma aka tabbatar da ganin jaririn watan sallah. Idan mutum ya
musulunta ko aka haifi yaro kafin faɗuwar rana, to, wajibi ne a fitar masa da wannan Zakkar . Amma idan hakan ya
faru bayan faɗuwar rana, to zakkar bata wajabtaba .
Waɗanda Zakkar take
wajaba akansu
1. Kowani Musulmi – Maza da Mata Yara da manya(masu Yanci ba
abyiba) da Bayi Maza da Mata, Manya da yara.
2. Masu dama – Wanda ke da Isasshen abinci shi da iyalansa a wannan yinin kuma har
yaragu.
3. Mai daukar nauyin wasu – Idan mutum yana ciyar da
matarsa, ‘ya’yansa, iyayensa da sauran ‘yan uwansa da ke ƙarƙashin kulawarsa,
to, zai fitar da Zakkar a
madadinsu.
Adadin da ake
bayarwa
Adadin Zakkar shi ne
sa'i ɗaya (1 صاع) na abinci, wanda
yake daidai da kimanin 3kg na shinkafa, gero, alkama ko duk wani abinci da ake
amfani da shi a cikin wannan yankin.
Nau'in Abincin da ake
bayarwa
Ana bayar da Zakkar ne Nau’in abinci irin su:
- Shinkafa
- Alkama
- Gero
- Dawa
- Wake
- Ko Duk wani nau'in abinci da mutane ke amfani da shi a matsayin
abincin yau da kullum a ƙasarsu.
Anfani ko Fa'idar Zakkar
Fitar
1. Tsarkake mai azumi daga kura-kuran da suka faru yayin
azumi.
2. Taimakawa Talakawa domin sanyasu farin ciki a Ranar
sallah.
3. Haɗa kan al’umma ta hanyar tallafa wa marasa galihu.
Zakkar Fidda akai ibada ce mai muhimmanci da ke tabbatar da
jin ƙai da haɗin kai tsakanin Musulmai. Don haka, dole ne a bayar da ita kafin
sallar Idi domin ta cika manufarta.
Allah yabamu Ikon Bayarwa
Muhammad Idris Kumbash
Post a Comment