HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDIL FIDRI

 


 

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, da salati da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad, da iyalansa da sahabbansa gaba ɗaya. 

 

 Ma’anar Idi 

Idi kalma ce da ke nufin kowace rana da ake maimaitawa a kai a kai. Yin binkin Idi  alamace dake nuna al’adu ko addinin  na mutane  daban-daban, ko da kuwa sun kasance Yahudawa, Kiristoci, masu bautar gumaka, ko wani  Idi na da alaƙa da dabi’a da addini na mutum, domin kowane mutum yana son ya sami lokaci na farin ciki da taruwa da ‘yan uwansa. 

Idin wasu al’ummar da ba musulmi ba su kan shafi abubuwa na rayuwar duniya, kamar farkon shekara, lokacin shuka, sauyin yanayi, kafa mulki, ko nadin shugaba. Hakanan suna da Idi na addini, kamar yadda Kiristoci suke da idodinsu, ciki har da ranar da suka ce an saukar da abinci daga sama ga Annabi Isa (A.S), da Kirsimeti, da Ranar Godiya, da Ranar Kyauta. 

Maguzawa kuma suna da Idinsu kamar idi na "Mehragan" da "Nayruz". Haka nan ‘yan Shi’a suna da idinsu na "Idin Ghadir", wanda suke zargin cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ba Ali (R.A) mulki a wannan rana. 

 

Musulmai da Idodinsu 

Annabi Muhammad (S.A.W) ya tabbatar da cewa musulmai suna da idodi biyu kawai: Idin Fitr da Idin Layya. Wannan yana nuna cewa bai halasta ga musulmai su yi koyi da kafirai wajen yin idodinsu ba, ko da a cikin abinci, sutura, kunna wuta, ibada, ko wasa. Idodin kafirai da bidi’a duk haram ne, ciki har da Kirsimeti, Ranar Haihuwa, Ranar Mahaifa, Ranar Ma’aikata, da sauransu. 

Dalilin wannan shi ne hadisin Anas (R.A) wanda ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya zo Madina, sai ya tarar da mutane suna da wasu ranaku da suke wasa a cikinsu. Sai ya ce, ‘Mene ne waɗannan ranaku?’ Sai suka ce, ‘Muna yin wasa a cikinsu tun zamanin Jahiliyya.’ Sai Manzon Allah ya ce, ‘Allah ya maye maku da wasu mafi alheri daga gare su: Ranar Layya da Ranar Fitr.’" (Abu Dawud 1134). 

 

 Dokokin Idi 

 Haramcin Azumin Ranar Idi 

Bai halasta a yi azumi a ranakun Idi ba. A hadisin Abu Sa’id Al-Khudri (R.A), ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya hana yin azumi a ranar Idin Fitr da Idin Layya." (Muslim 827). 

 

Hukuncin Sallar Idi 

Malamai sun bambanta a kan wajabcin Sallar Idi: 

- Mazhabar Hanafiyya da Sheikhul Islam Ibn Taymiyya sun ce wajibi ne. 

- Mazhabar Hanbaliyya sun ce Fardu  Kifaya ce (wasu na daukewa wasu). 

- Malaman Malikiyya da Shafi’iyya sun ce sunnah ce mai karfi. 

Duk da haka, ya kamata musulmi su yi kokari wajen halartar wannan sallah domin samun lada da koyi da Annabi (S.A.W). 

 

 Lokacin Sallar Idi 

Yawancin malamai sun ce ana yin Sallar Idi bayan fitowar rana da dan lokaci har zuwa lokacin azahar. 

 

 Yadda Ake Sallar Idi

Sallar Idi raka’a biyu ce: 

- A raka’a ta farko, ana yin Kabar bari guda bakwai 7 bayan takbiratul ihram. 

- A raka’a ta biyu, ana yin kabar bari guda biyar 5 kafin fara karatu. 

 

Hakanan, yana da kyau liman ya karanta surorin: 

- "Qaf" da "Al-Qamar" (Muslim 891) 

- "Sabbihisma" da "Al-Ghashiya" (Muslim 878) 

 

Zuwan Mata  Sallar Idi

 

A cikin hadisin Ummu ‘Atiyya (R.A), Annabi (S.A.W) ya umarci mata da ‘yan mata su fita zuwa Sallar Idi, har da masu haila, amma su zauna daga gefen masallaci. (Bukhari 324). 

 

Haka nan, idan mace ba ta da hijabi, sai wata ta ara mata domin ta halarci wannan ibada mai girma. 

 

 Sunnonin Ranar  Idi

 

1.  Ana Sallar Idi ne kafin huduba – Manzon Allah (S.A.W) ya fara da sallah kafin yin huduba. 

2. Ana iya tafiya daga huduba – Idan mutum yana yanada Uzuri, yana iya tafiya bayan sallar idi ba tare da sauraron huduba ba, amma jin hudubar abune me muhimmanci.

3. Ba a  jinkirin yin sallah, se dai wasu malaman suna ganin anso jinkirta sallar Idil fitr saboda fitar da Zakatil fidir – A lokacin Annabi (S.A.W), ana yin sallar idi da wuri. 

4. Ba a Yi Nafila Kafin ko Bayan Sallar Idi 

A hadisin Ibn Abbas (R.A), ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya fita a ranar Idi ya yi raka’a biyu, bai yi sallar nafila ba kafin su ba, kuma bai yi salla bayan su ba." (Abu Dawud 1159).  

5.Wanka kafin tafiya sallar Idi 

Daga cikin laduban sallar Idi akwai yin wanka kafin tafiya masallaci. An tabbatar a cikin Muwatta' cewa Abdullah bn Umar yana yin wanka a ranar Idi kafin fita zuwa masallaci (Muwatta' 428). 

Haka nan, an rawaito daga Sa'id bn Jubair cewa ya ce: "Sunnonin Idi guda uku ne: tafiya a kafa, yin wanka, da cin abinci kafin fita." 

Sheikh Nawawi (rahimahullah) ya ambaci cewa malamai sun yi ittifaki kan mustahabcin yin wanka don sallar Idi, kamar yadda ake yin wanka don sallar Jumu'a da sauran taruka na ibada. 

6.Cin abinci kafin fita a Idil fidri 

Daga cikin sunnonin Idi akwai cin 'ya'yan dabino kafin fita zuwa sallar Idi. An rawaito daga Anas bn Malik cewa Manzon Allah () ba ya fita ranar Idi har sai ya ci dabino.(Bukhari 953).    

Dalilin hakan shi ne nuna cewa azumin watan Ramadan ya kare, da kuma kauce wa cigaba da azumi bisa kuskure. Idan mutum bai samu dabino ba, to yana iya cin wani abincin . Amma a ranar Idi Al-Adha, mustahabbi ne a jira har sai an ci daga dabbar layyar ka hadaya. 

7.Takbiri a ranar Idi 

Daga cikin sunnonin ranar Idi akwai yin takbiri kamar yadda Allah Ya ce a cikin Al-Qur’ani: 

"Kuma ku cika adadin kwanaki, kuma ku yi tasbihi ga Allah bisa ga shiryarwarsa a gare ku, domin ku gode." (Al-Baqara 2:185). 

 An rawaito daga Ibn Umar cewa yana fitowa a ranar Idi yana takbiri har sai  liman ya fito. Haka nan, Ibn Abi Shayba da Imam Malik sun rawaito cewa mutane a zamanin sahabbai suna yin takbiri daga gidajensu har zuwa masallaci, sannan su dakata idan liman ya fito. 

 Lokacin yin takbiri na ranar Idi Al-Fitr yana farawa daga daren Idi har sai liman ya fito don sallah. 

 

Siffar takbiri: 

An rawaito daga Ibn Mas’ud cewa yana cewa: 

_"Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illa Allah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, wa lillahil hamd."  

 

8.Gaisuwa da taya murna

Daga cikin laduban Idi akwai gaisawa da addu’o’i masu kyau kamar: 

"Taqabbalallahu minna wa minkum" (Allah ya karɓi ibadunmu da na ku). 

An rawaito daga Jabir bn Nufair cewa sahabbai suna fadin haka idan sun hadu a ranar Idi. Malamai sun halatta hakan, domin yana daga cikin kyawawan al’adu da ke karfafa zumunci a tsakanin musulmi. 

 

9.Yin kwalliya da yin ado a ranar Idi 

Daga cikin sunnonin Idi akwai sanya kaya masu kyau. An rawaito cewa Manzon Allah () yana da wata riga da yake sanyawa a ranakun Idi da Jumu’a (Ibn Khuzayma 1765). Haka nan, an tabbatar cewa Ibn Umar yana sanya mafi kyawun kayansa a ranar Idi. 

Amma ga mata,  wajabine  su guji  yin ado mai jan hankali, amfani da turare, da kuma sanya tufafin da za su janyo hankalin maza. Saboda fitarsu ibada ce, ba don nuna ado ba. 

 

Hukuncin sauraron hudubar Idi

Malamai sun bayyana cewa sauraron hudubar Idi yana da kyau, amma ba wajibi ba ne kamar yadda hudubar Jumu’a take. 

 An rawaito cewa Manzon Allah () ya ce: 

"Mun yi huduba, wanda yake so zai zauna, wanda yake so zai tafi." 

Sheikh Ibn Uthaymeen ya ce idan mutum yana wurin huduba, to dole ne ya yi shiru ba tare da ya shiga hira da wani ba, domin kada ya katse hankalin masu sauraro. 

 

10.Fita ta wata hanya da dawowa ta wata hanya 

An rawaito daga Jabir bn Abdullah cewa Manzon Allah () yana fita sallar Idi ta wata hanya, sannan ya dawo ta wata hanya daban (Bukhari 986). 

 

Daga cikin hikimomin hakan akwai: 

- Don alamta shaharar sallar Idi a cikin gari. 

- Don bayar da damar yin sallama dab sada zumunci da wasu mutane. 

- Don yin ibada a hanyoyi daban-daban, domin ana cewa ƙasa za ta yi shaida da ayyukan da aka aikata a kanta. 

 

Guje wa wasu kurakurai a ranar Idi 

1. Raya daren Idi da ibada musamman daren Idi: Babu hadisin da ke tabbatar da hakan, don haka bai kamata a dauki hakan a matsayin ibada ta musamman ba. 

2. Cakuduwa da haduwa tsakanin maza da mata a wajen sallah: Wannan yana haifar da fitina, kuma bai dace ba. Mata su guji kwalliya da fitowa da ado mai jan hankali. 

3. Rowa ko Rashin sada zumunci: Akwai ladubban Idi da suka hada da kyautata wa 'yan uwa da sada zumunci. 

 

Fadakarwa

Idin Musulmi alama ce ta addini da ibada, ba al’ada kawai ba. Ya kamata musulmai su kiyaye yadda suke gudanar da idinsu, ba tare da kwaikwayon kafirai ko bidi’a ba. Allah ya sa mu dace!


MUHAMMAD IDRIS KUMBASH

Post a Comment

Previous Post Next Post