Falalar Azumin Kwanaki Shida na Shawwal




Falalar Azumin Kwanaki Shida na Shawwal 

 

Tambaya 

Mene ne hukuncin azumin kwanaki shida na Shawwal, shin wajibi ne? 

 

Amsa a Taƙaice 

Yin azumin kwanaki shida na Shawwal(Sitta shawwal) Sunnah ce da ake so a yi, ba wajibi ba ne. Yin azumin waɗannan kwanaki shida bayan Ramadan yana daidai da yin azumi na shekara gaba ɗaya. Hakan yana kuma cike duk wani gibi ko kura-kurai da aka samu a azumin Ramadan. 

 

Cikakken Bayani 

Azumin kwanaki shida na Shawwal (Sitta Shawwal)bayan azumin Ramadan sunnah ce mai karfi, ba wajibi ba. Ana so musulmi ya yi wannan azumin saboda girman lada da falalarsa, domin wanda ya yi  ana rubuta masa ladan azumin shekara gaba ɗaya. 

 

An tabbatar da wannan daga hadisin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda Abu Ayyub Al-Ansari (RA) ya rawaito, inda Manzon Allah (SAW) ya ce: 

 

"Duk wanda ya yi azumin Ramadan, sannan ya bi shi da azumin kwanaki shida na Shawwal, kamar yayi azumin shekara ne gaba ɗaya." 

(Hadisin Muslim, Abu Dawud, Tirmizi, Nasa'i da Ibn Majah) 

 

Annabi (SAW) ya bayyana hikimar hakan inda ya ce: 

 

"Wanda ya yi azumi kwanaki shida bayan Idi, yana cike azumin shekara gaba ɗaya: domin duk wanda ya kawo kyakkyawan aiki, yana da lada goma na irin sa."

(Hadisin Nasa’i da Ibn Majah, kuma an tabbatar da shi a Sahih Al-Targhib wa Al-Tarhib 1/421)  

Ibn Khuzaymah kuma ya rawaito hadisi da lafazin: 

"Azumin watan Ramadan yana daidai da lada na wata goma, kuma azumin kwanaki shida na Shawwal yana daidai da wata biyu, wanda hakan ke cika ladan azumin shekara gaba ɗaya."

Mafi yawan malamai daga mazhabar Hanbali da Shafi’i sun bayyana cewa yin azumin kwanaki shida na Shawwal yana daidai da azumin shekara gaba ɗaya, kamar yadda aka ambata a hadisan. 

 

Fa'idodin Azumin Kwanaki Shida na Shawwal 


- Cike duk wani gibin da ke cikin azumin Ramadan, kamar yadda ake cike gibin salloli da nafila. 

- Karin lada da kusanci da Allah. 

- Koyon daidaita kai da ci gaba da ibada bayan Ramadan, ba tare da dakatar da ayyukan alheri ba. 

Annabi (SAW) ya ce game da cike gibin ayyukan farilla: 

 

"Abu na farko da za a yi hisabi akansa ranar Alƙiyama shi ne sallah. Idan sallar bawa ta cika, za a rubuta masa cikakkiya, idan kuwa akwai gibi, to, za a ce ku duba ko yana da nafila. Idan yana da nafila, sai a cike gibin sallarsa da ita, sannan a ci gaba da duba sauran ayyukan sa." 

(Hadisin Abu Dawud) 

Hakan yana nuna cewa ana amfani da nafila wajen cike gibin farilla, wanda hakan yana cikin hikimar azumin kwanaki shida na Shawwal.


MUHAMMAD IDRIS KUMBASH

Post a Comment

Previous Post Next Post