Yadda Ake Yin Sallar Istihara da Lokacin yin Addu'a
Hukuncin Sallar Istihara:
- Sallar Istihara sunnace mai karfi da ta tabbata daga Annabi (SAW). Ita ce hanya ta neman Zabi a wajan Allah (SWT) a cikin al’amuran da Musulmi yake cikin shakku ko rashin tabbaci da rashin natsuwa akansu.
Yadda Ake Yin Sallar Istihara:
-
Niyya:
Mutum ya yi niyyar yin Sallar Istihara a zuciyarsa ba tare da bayyana ta da baki ba. -
Sallar:
- A yi sallah raka’a biyu kamar kowace nafila.
- A karanta Fatiha da kowace sura da tasamu a kowace raka’a.
-
Addu’a Bayan Sallama:
Bayan an idar da sallah da sallama, sai mutum ya daga hannayensa ya yi addu’ar Istihara kamar yadda ta zo daga Annabi (SAW).
Addu’ar Istihara:
“Allahumma inni astakhiruka bi’ilmika, wa astaqdiruka biqudratika, wa as’aluka min fadlika al-‘azim. Fa’innaka taqdiru wa la aqdir, wa ta’lamu wa la a’lam, wa anta allamul-ghuyub.
Allahumma in kunta ta’lamu anna hadha al-amr (a faɗi abin da ake so kamar aure, tafiya, aiki, ko wani abu) khayrul li fi dini wa ma’ashi wa aqibati amri, faqdirhu li, wa yassirhu li, thumma barik li fihi.
Wa in kunta ta’lamu anna hadha al-amr sharrul li fi dini wa ma’ashi wa aqibati amri, fasrifhu anni, wasrifni anhu, waqdir li al-khayr haithu kan, thumma ardini bihi.”
Lokacin Addu’a:
- Ana yin addu’a bayan an kammala sallah da sallama, kamar yadda aka rawaito daga Annabi (SAW) a hadisin da Imam Bukhari ya kawo.
Muhimman Bayanan da Ya Kamata a Sani:
- Istihara anayintane akan al’amuran da suka halatta kuma mutum yake shakka kansu, Ba a yin ta a kan abubuwan da aka haramta ko aka wajabta.
- Idan mutum bai samu natsuwa ba bayan yin Sallar Istihara, zai iya maimaitawa.
- Bayan yin Istihara, ya kamata mutum ya dogara ga Allah tunda yariga yaba Allah zabi sannan ya yi abin da ya ga ya dace.
Fadakarwa
kada wani ya yaudareka dacewa wai zeyimaka istihara, istihara kai zakayima kanka da kanka bawani zeyimakaba saboda haka sunnah ta koyar, Amma kaiya neman dan uwanka musulmi yatayaka Addu'a Akan wani Abu da kake nema.
Allah ya ba mu ikon yin abin da zai zama alheri a gare mu, amin.
Muhammad Idris Kumbash
.jpg)
Post a Comment