Hukunce Hukuncen Azumi




 

 Falalar Watan Ramadan


- Ramadan wata ne na alheri da albarka. Allah ya fifita shi da falaloli masu yawa da kuma wasu siffofi na musamman, daga ciki:

A cikin watan aka saukar da Al-Qur'ani.

Ana buɗe ƙofofin Aljanna a cikinsa.

Ana rufe ƙofofin Wuta a cikinsa.

Ana ɗaure shaiɗanu a cikinsa.

Allah yana gafarta zunubai da kurakurai a cikinsa.

Akwai daren Lailatul Qadr a cikinsa, wanda ya fi wata dubu alheri.

Allah yana 'yanta bayi daga Wuta a kowace dare a cikinsa.


 Rukannan Azumi


- Azumi yana da ginshiƙai biyu: su ne niyya da kuma kame baki daga cin abinci ko shan abin sha (imsaki).

- Niyya: ita ce kayi nufin  kusanci da Allah ta hanyar ibada,  a zuciya akeyinta, ba a    furta niyya, kuma furta niyya bidi’a ce, ko da kuwa mutane suna ganin hakan abu ne mai kyau.

- Dole ne a tabbatar da niyya da nufin azumi da gaske, kuma a yi wannan niyya kafin alfijir idan azumin Ramadhan ne, ba na nafila ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post