Hukuncin wanda ya zagi Annabi (SAW)

 







Hukuncin wanda ya zagi Annabi (SAW)

Malaman Musulunci sun tafi  a kan ra'ayi guda cewa duk wanda ya zagi Annabi Muhammadu (SAW), kafiri ne, kuma jinin sa ya halatta. Amma malamai sun yi sabani kan ko ana iya karɓar tuba daga irin wannan mutum. Wasu sun ce idan ya tuba tuba ta gaskiya, za a karɓa, jinin sa kuma zai zamto haramun – wato ba za a kashe shi ba. Wasu kuma sun ce, tuba ba za ta amfane shi ba, dole a kashe shi. Idan kuwa tubar ta gaskiya ce, Allah zai iya gafarta masa a lahira.

Sheikh Muhammad Salih Al-Munajjid daga kasar Saudiyya ya ce:

Amsar wannan tambaya na bukatar mu fahimci abubuwa biyu:

Na farko: Mene ne hukuncin wanda ya zagi Annabi (SAW)?

Dukkan malaman Musulunci sun amince cewa duk musulmin da ya zagi Annabi Muhammadu (SAW) ya zama kafiri kuma yayi ridda – wato ya fita daga Musulunci. Hukuncinsa shi ne a kashe shi.

Wannan magana ta tabbata daga littafi mai tsarki (Al-Qur’ani) da kuma hadisan Annabi (SAW).

Ga Dalili Daga Al-Qur’ani:

A cikin suratul Tawba aya ta 65-66, Allah ya ce:

(Idan ka tambaye su, za su ce: "Mun yi wasa ne kawai da zance." Ka ce: "Shin da Allah da ayoyinSa da kuma ManzonSa kuke yi wa izgili? Kada ku nemi uzuri. Kun riga kun kafirce bayan imani.”)

Wannan aya tana nuna cewa duk wanda ya yi izgili ko wulakanta Allah ko ayoyinSa ko Annabi (SAW), ya zama kafiri. Idan izgili kafirci ne, to zagi ya fi tsanani.

Ga Dalili Daga Hadisan Annabi (SAW):

A wani hadisi daga Ali (RA), wata mata Bayahudiya tana zagin Annabi (SAW), wani mutum ya shake ta har ta mutu. Annabi (SAW) bai hukunta shi ba, ya ce ba zaabada   diyya ba saboda mutuwarta.

A wani hadisin daban daga Ibn Abbas (RA), wani makaho yana da wata baiwa da ke zagin Annabi (SAW). Yana hana ta, amma tana cigaba da hakan. Wata rana ya kashe ta. Annabi (SAW) ya ce: “Ku sani, jinin ta ya halatta – ba a yi kuskure ba da aka kashe ta.”

Wannan yana nuni da cewa zagin Annabi babban laifi ne wanda ke sa a kashe wanda ya aikata shi.

Yana  yiyuwa cewa wannan matar ba musulma bace – domin da ace musulma ce, da hakan ya sa ta fita daga Musulunci gaba daya, kuma bai kamata mijinta ya ci gaba da zama da ita ba.


MUHAMMAD IDRIS KUMBASH

Post a Comment

Previous Post Next Post