Azumi da Falalarsa

1- Azumi: Shine  Yin kusanci ga Allah Ta'ala ta hanyar nisantar ci da sha da jima'i daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana da niyyar bautawa Allah .


2- Azumi yana da falaloli masu yawa da mai azumi zai amfana da su a rayuwarsa da bayan mutuwarsa; daga cikinsu:


1- Azumi hanya ce zuwa ga imani da tsoron Allah.


2- Azumi garkuwa ce da take kare rai daga sha'awoyi.


3-Azumi garkuwa ce da bawa zai tsira da ita daga wuta a ranar kiyama.


4- Azumi kaffara ne ga zunubai da kura-kurai.


5-Azumi mai yin shafa’a ne ga mai azumi a ranar kiyama.


6-masu azumi suna da ƙofa ta musamman a aljanna da ake kira "Ar-Rayyan."

 

7-warin bakin mai azumi ya fi ƙamshi a wurin Allah a ranar kiyama fiye da ƙamshin turaren misk.


8- mai azumi yana da farin ciki biyu: farin cikin lokacin buda-bakinsa da farin cikin lokacin haduwa da Ubangijinsa.


9-mai azumi za a ba shi ladansa a ranar kiyama ba tare da lissafi ba.

Muhadu a Darasi na gaba 

📝Muhammad Idris  kumbash


Post a Comment

Previous Post Next Post