Nau’ikan Azumi
Gida nawa Azumi yakasu?
Munada Azumi Nau’i 2
- Azumi ya kasu gida biyu gasu kamar haka:
1-Muna da Azumin Farilla
2-Muna da Azumin Nafila.
=Shikuma Azumin Farilla yakasu gida uku:
1-Azumin Bakance (nathar), kamar kace Idan Allah yasa naci Jarabawa to zanyi Azumi 3 tofa
muddin kasamu nasara A Jarabawarka wannan Azumin yazama farilla Akanka.
2-Azumin Kaffara, kamar kaffarar Rantsuwa,kisan kai bisa kuskure da dai sauransu
3-Azumin Watan Ramadan wanda shine zamuyi magana akansa
Shar’ancin Azumin Ramadan
- Allah ya wajabta Azumin Ramadan a cikin Al’qur’ani inda yace:
(Ya ku wadanda kuka yi imani! An wajabta muku yin azumi kamar yadda aka wajabta wa
Al'ummar da sukazo kafin ku, don ku zama masu tsoran Allah)
(Suratul Baqara: 183)
Da kuma inda yace:
(Duk wanda watan Ramadan yasameshi (daransa da Lafiyarsa)to ya yi azumi)
(Suratul Baqara: 185)
=Dukkan malamai sun hadu akan cewa Azumin Ramadan farilla ne daga cikin farillan Addinin
musulunci, kuma yana daya daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci, duk wanda ya musanta
wajabcin Azumin Ramadan ya kafirta kuma ya fita daga Musulunci.
= Ana tabbatar da shigowar watan Ramadan ta hanyar ganin jinjirin wata, koda ganin mutum
dayane Adali wato mutumin kirki, ko kuma idan watan yacika kwanaki 30 na watan Sha’aban.
=Wajibi ne yin Azumin Ramadan ga kowani baligi,lafiyayye kuma mai hankali, kuma mazaunin gida ba matafiyi ba, banda mace mai al’ada ko mai jinin haihuwa.
Wato mace me Al’ada ko me jinin Haihuwa wajabcin Azumi yafadi akanta yayinda take Al’ada
ko jinin haihuwa amma zata rama bayan tagama Kuma bayan Ramadan
Muhadu A Darasi nagaba
Muhammad Idris Kumbash
Post a Comment