Wankan Janaba

 


 Wankan  janaba a Musulunci:

                                Menene Janaba?

 

=Janaba a yaran larabci yana nufin NISANTAR WANI ABU

Janaba wajan Malaman Fiqhu shine fitar maniyyi ko kuma haduwar Azzakari da farji,

 Ankirashi da janabane saboda niasantar sallah damutum zeyi idan janabar tasameshi

 harseyayi wanka.

 

  Me ke kawo janaba?

 

1. Fitar maniyyi (a mafarki ko a zahiri). 

2. Saduwa tsakanin namiji da mace, ko da ba a samu fitar maniyyi ba. 

 

Karkasuwan wankan janaba

 

=Wankan janaba ya kasu gida 2

1- A kwai takai tacce: Takaitaccen wankan janaba shine wankan janaba da mutum zeyishi don

 sauke wajibin dake kansa da gusar da kazantar jikinsa batare da yayi wasu sunnoni da

 mustahabbaiba kuma wankansa yayi sedai bezoda sunnoni da mustahabbaiba

 

Yanda ake Takaitaccen wankan janaba

 

=Mutum zeyi niyyar wankan janaba ya kurkure bakinsa ya shaqi ruwa ahanci ya fyace se

   yawanke dukkan jikinsa gabaki daya ya tabbatar ko ina yasamu ruwa shikenan, amma

   wannan wankan baayin sallah dashi kamar yanda mukayi bayani tunda ba alwala acikinsa.

 

2- Akwai cikakken wankan janaba

Yadda Ake cikakken  Wankan Janaba 

Sharuddan Wankan Janaba

 Kafin wankan janaba ya inganta, dole se ya cika wasu sharudda:

1- Niyya: Fada a zuciya cewa za ka yi wankan janaba domin tsarkake kanka.   

2-Kawar da najasa: Dole ne ka tabbatar babu najasa a jiki kafin ka fara, Tahanyar wanke duk

 wata najasa tajiki.

 

 Yanda ake Wankan Janaba

Manzon Allah (SAW) ya bayyana yadda ake wankan janaba, kuma an rarraba shi zuwa

 matakai kamar haka: 

1- Wanka Na Sunnah (Yadda Manzon Allah Yake Yi)

Mataki 1: Ka fara da niyya. 

Mataki 2: Ka wanke hannunka sau uku. 

Mataki 3: Ka yi alwala kamar yadda ake alwala na sallah, amma bazaka wanke kafarkaba se

 a karshen wankanka.

Mataki 4: Ka zuba ruwa a kanka sau uku, ka tabbata ya isa ga fatar kai, wato ka cuda kanka

 sosai 

Mataki 5: Ka wanke dukkan jikin ka da ruwa kafara da bangaran dama sannan hagu,ka

 tabbata babu wani bangare da ruwa bai kai ba. 

 

Abubuwan da zaalura dasu yayin wankan janaba

1-Amfani da ruwa mai tsarki. 

2-A tabbatar koina yasamu ruwa ajiki. 

3-Yin niyya kafin farawa.

4-Kada a manta da tsaftace wuraren da aka fi mantawa, kamar:

  Bayan kunne.

  Kasan yatsun ƙafa.

  Kasan gashi mai yawa, da tsefe gemu ga maza

  Wanke dugadugin kafa

 

kucigaba Da kasancewa tare damu domin samun sabbin darussa


✎Muhammad Idris Kumbash

 

 

 

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post