Falalar Azumin Ranar Arfa



 Falalar Azumin Ranar Arfa


An rawaito a cikin Sahih Muslim da wasu, cewa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

“Azumin ranar Arafah ina fatan Allah zai gafarta wa wanda ya yi ta, zunuban shekarar da ta gabata da kuma shekarar me zuwa.”

Wannan hadisin yana nuni a bayyane cewa azumin ranar Arafah yana kankare zunuban shekaru biyu.

Ana so a yawaita ayyukan Alheri irin su sallar nafila, azumi, sadaka, ambaton Allah da sauransu a cikin ranakun goma na farko na Zul-Hijjah gaba ɗaya, musamman ma a ranar Arafah.

A cikin wani hadisi, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

"Babu wasu kwanaki da ayyukan alheri su fi soyuwa ga Allah fiye da wadannan kwanakin," ma’ana ranakun goma na farkon watan zulhijjah.

Sahabbai suka ce: “Ko jihadi a hanyar Allah ma?”

Sai ya ce: “Ko jihadi a hanyar Allah ma, sa

i dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, bai dawo da komai daga ciki ba.”

(Hadisin nan yana cikin Sahih Bukhari)


Allah yasa mudace


Muhammad Idris Kumbash

Post a Comment

Previous Post Next Post