TAMBAYA
Shin ya halatta ga Musulmi ya ci abincin da kiristoci ko wanda ba musulba suka shirya a ranakun
bukukuwan su(kirsimeti), ko ya karɓi kyauta daga gare su saboda tayasu murnar bukukuwan su?
AMSA
1-Sharaa ta halattawa musulmi cin
abincin kiristoci ko amsar kyauta daga garesu
haka kaima an halattama kabasu abinci ko kayi musa kyauta ko
muamalattarsu ko kasuwanci tare dasu abisa tsari na musulunci, amma gameda cin
abincinsu ko amsar kyautuka daga garesu lokutan bukukuwansu na Ibada ga fatawar
malamai daga LAJNATUD DAIMA
2- “Ba ya halatta ga Musulmi ya ci daga cikin abincin da Yahudawa ko Nasara ko mushrikai suka shirya don bukukuwan su na Ibada, kuma ba ya halatta ga Musulmi ya karɓi kyauta daga gare su saboda bukukuwan su na Ibada. Domin yin hakan yana nuna girmamawa da tayasu murna, da kuma yin aiki tare da su wajen bayyana al'adun addininsu, tallata bid'arsu, da kuma shiga farin cikin da suke yi a ranakun bukukuwan su wanda Hakan kuma ya sabawa sharaar mususlunci.”
Saboda manzan Allah (saw) yace:(
mutum yana tare da wanda yakeso Ranar Alqiyama).
A wani hadisin kuma yace:( wanda yayi
kamanceceniya da wasu mutane to yana cikinsu).
Bisa waannan dalilan yazama
Haramunne tayasu ko taimakonsu akan bukukuwansu
ko ayyukan da sukashafi ibadunsu ko tayasu farin ciki a irin wannan
lokaci.
Allah yasa mudace.
Muhammad Idris Kumbash
Jazakhallahu Khairan
ReplyDeleteameen ya Rab
ReplyDeletePost a Comment